Irm 51:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Zan aika da masu casawa zuwaBabila, za su casa ta,Su bar ƙasarta kango.Za su kewaye ta a kowane sashiA wannan ranar masifa.

3. Kada ku bar maharbi ya yi harbi dabakansa,Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa,Kada ku rage samarinta,Ku hallaka dukan sojojinta.

4. Za su fāɗi matattu a ƙasarKaldiyawa,Za a sassoke su a titunansu.”

5. Allah na Isra'ila da Yahuza,Ubangiji Mai Runduna, bai yashesu ba,Ko da yake sun yi wa Mai Tsarki naIsra'ila zunubi.

6. Ku gudu daga cikin Babila,Bari kowa ya ceci ransa,Kada a hallaka ku tare da ita,Gama a wannan lokaci Ubangiji zaisāka mata,Zai sāka mata bisa ga alhakinta.

Irm 51