18. Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwane kawai,Za su lalace a lokacin da za ahukunta su.
19. Amma wanda yake wajen Yakubu bahaka yake ba,Domin shi ne ya halicci dukanabu,Isra'ila kuwa abin mallakarsa ne,Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.
20. Ubangiji ya ce,“Kai ne guduma da kayan yaƙina,Da kai ne na farfasa ƙasashenduniya,Da kai ne na hallaka mulkoki.
21. Da kai ne na karya doki damahayinsa,
22. Da kai ne na farfasa karusa damahayinsa.Da kai ne na kakkarya mace danamiji,Da kai ne na kakkarya tsoho dasaurayi,Da kai ne na kakkarya saurayi dabudurwa,
23. Da kai ne na kakkarya makiyayi dagarkensa,Da kai ne na kakkarya manoma dadawakan nomansa,Da kai ne na kakkarya masu mulkida shugabanni.”
24. Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.
25. Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse maihallakarwa,Wanda ya hallaka duniya duka.Zan miƙa hannuna gāba da kai,Zan mirgino da ƙasa dagaƙwanƙolin dutse,Zan maishe ka ƙonannen dutse.