14. Ubangiji Mai Runduna ya rantse dazatinsa, ya ce,“Hakika zan cika Babila da mutanekamar fāra,Za su kuwa raira waƙar nasara akanta.”
15. Ubangiji ne ya halicci ƙasa daikonsa,Ya kafa duniya da hikimarsa,Ya kuma shimfiɗa sammai dafahiminsa.
16. Bisa ga umarninsa ruwan da yakesamaniya yakan yi ruri,Yakan sa gajimare su tashi dagaƙarshen duniya,Yakan sa walƙiya ta walƙata cikinruwan sama,Yakan sa iska ta haura daga cikintaskokinsa.
17. Kowane ɗan adam wawa ne, mararilimi,Kowane maƙerin zinariya kuma zaisha kunya daga wurin gumakansa,Gama siffofinsa na ƙarya ne, banumfashi a cikinsu.
18. Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwane kawai,Za su lalace a lokacin da za ahukunta su.
19. Amma wanda yake wajen Yakubu bahaka yake ba,Domin shi ne ya halicci dukanabu,Isra'ila kuwa abin mallakarsa ne,Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.
20. Ubangiji ya ce,“Kai ne guduma da kayan yaƙina,Da kai ne na farfasa ƙasashenduniya,Da kai ne na hallaka mulkoki.
21. Da kai ne na karya doki damahayinsa,
22. Da kai ne na farfasa karusa damahayinsa.Da kai ne na kakkarya mace danamiji,Da kai ne na kakkarya tsoho dasaurayi,Da kai ne na kakkarya saurayi dabudurwa,
23. Da kai ne na kakkarya makiyayi dagarkensa,Da kai ne na kakkarya manoma dadawakan nomansa,Da kai ne na kakkarya masu mulkida shugabanni.”
24. Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.
25. Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse maihallakarwa,Wanda ya hallaka duniya duka.Zan miƙa hannuna gāba da kai,Zan mirgino da ƙasa dagaƙwanƙolin dutse,Zan maishe ka ƙonannen dutse.
26. Ba za a sami dutsen yin kusurwa, kona kafa harsashen gini a cikinkaba,Amma za ka zama marar amfani harabada.”
27. Ku ta da tuta a duniya,Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho,Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙida ita,Ku kirawo mulkokin Ararat, da naMinni, da na Ashkenaz, su yi yaƙida ita.Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zaishugabanci yaƙin da za a yi da ita,Ku kawo dawakai kamar fāra.
28. Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita,Sarakunan Mediyawa, da masumulkinsu, da shugabanninsu,Da kowace ƙasar da take ƙarƙashinmulkinsu.
29. Duniya ta girgiza, tana makyarkyatasaboda azaba,Gama nufin Ubangiji na gāba daBabila ya tabbata,Nufinsa na mai da ƙasar Babilakufai, inda ba kowa.