Irm 51:11-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ku wasa kibau, ku cikakwaruruwanku!Ubangiji ya ta da ruhun sarakunanMediyawa,Domin yana niyyar hallaka Babila.Gama Ubangiji zai yi ramuwasaboda Haikalinsa.

12. Ku ta da tuta don a faɗa wa garunBabila,Ku ƙarfafa matsara,Ku sa su su yi tsaro,Ku kuma sa 'yan kwanto!Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwaaikataAbin da ya faɗa a kan mazaunanBabila.

13. Ƙarshenki ya zo,Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa,Mai yawan dukiya.Ajalinki ya auka.

14. Ubangiji Mai Runduna ya rantse dazatinsa, ya ce,“Hakika zan cika Babila da mutanekamar fāra,Za su kuwa raira waƙar nasara akanta.”

15. Ubangiji ne ya halicci ƙasa daikonsa,Ya kafa duniya da hikimarsa,Ya kuma shimfiɗa sammai dafahiminsa.

Irm 51