Irm 50:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Jawabin da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kanBabila da ƙasar Kaldiyawa ke nan,

2. “Ku ba da labari ga sauranal'umma, ku yi shela,Ku ta da tuta, ku yi shela,Kada ku ɓuya, amma ku ce,‘An ci Babila da yaƙi,An kunyatar da Bel,An kunyatar da siffofinta,Merodak ya rushe,Gumakanta kuma sun ragargaje!’

3. “Wata al'umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.”

4. Ubangiji ya ce, “Sa'ad da lokacin nan ya yi, mutanen Isra'ila da na Yahuza za su zo tare, suna kuka, suna nemana, ni Ubangiji Allahnsu.

5. Za su tambayi hanyar Sihiyona, sa'an nan su bi ta, suna cewa, ‘Bari mu haɗa kanmu don mu yi madawwamin alkawari da Ubangiji, alkawari wanda ba za a manta da shi ba.’

6. “Mutanena sun zama kamar ɓatattuntumaki,Waɗanda makiyayansu suka bauɗarda su,Suka ɓata a cikin tsaunuka,Suna kai da kawowa daga wannandutse zuwa wancan.Sun manta da shingensu.

7. Duk waɗanda suka same su, suncinye su.Maƙiyansu suka ce, ‘Ba mu yi laifiba,’Gama sun yi wa Ubangiji laifi,wanda yake tushen gaskiya,Ubangiji wanda kakanninsu sukadogara gare shi.

8. “Ku gudu daga cikin Babila,Ku fita kuma daga cikin ƙasarKaldiyawa,Ku zama kamar bunsurai waɗandasuke ja gaban garke.

9. Ga shi, zan kuta manyan ƙasashedaga arewaSu faɗa wa Babila da yaƙi.Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, sucinye ta.Kibansu kamar na gwanayenmayaƙa neWaɗanda ba su komowa banza.

10. Za a washe Kaldiyawa,Waɗanda suka washe su kuwa za suƙoshi,Ni Ubangiji na faɗa.

11. “Saboda kuna murna, kuna farinciki,Ku da kuka washe gādona,Saboda kuma kuna tsalle kamarkarsana a cikin ciyawa,Kuna haniniya kamar ingarmu,

12. Domin haka za a kunyatar da Babilasosai, inda kuka fito.Za ta zama ta baya duka a cikinsauran al'umma,Za ta zama hamada, busasshiyarƙasa.

Irm 50