23. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Dimashƙu,“Hamat da Arfad sun gigice,Domin sun ji mugun labari,sun narke saboda yawan damuwa,Ba za su iya natsuwa ba.
24. Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi,Ta juya, ta gudu,Tsoro ya kama ta,Azaba da baƙin ciki sun kama takamar na naƙuda.
25. Ƙaƙa aka manta da sanannen birni,Birnin da take cike da murna?
26. A waccan rana samarinta za su fāɗi adandalinta.Za a hallaka sojojinta duka,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
27. Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu,Za ta kuwa cinye fādodinBen-hadad.”
28. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi,“Ku tashi zuwa Kedar,Ku hallaka mutanen gabas.
29. Za a kwashe alfarwansu dagarkunansu,Da labulan alfarwansu, da dukankayansu.Za a kuma tafi da raƙumansu,Za a gaya musu cewa, ‘Razana takewaye ku!’