19. “Ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji ya ce, ‘Kada ku tafi Masar.’ Ku tabbata fa na faɗakar da ku yau,
20. cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, ‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.’
21. A wannan rana kuwa na faɗa muku abin da ya ce, amma ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku a kan kowane abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.
22. Domin haka yanzu fa ku sani takobi, da yunwa, da annoba, su ne ajalinku a wurin can da kuke sha'awar ku zauna.”