Irm 40:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Yohenan ɗan Kareya kuwa, tare da dukan shugabannin sojojin da suke cikin sansani a karkara, suka zo wurin Gedaliya a Mizfa.

14. Suka ce masa, “Ko ka sani Ba'alis Sarkin Ammonawa ya aiko Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe ka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam, bai gaskata su ba.

15. Sai Yohenan ɗan Kareya ya yi magana da Gedaliya a Mizfa a asirce ya ce, “Ka bar ni in tafi in kashe Isma'ilu ɗan Netaniya, ba wanda zai sani. Don me shi zai kashe ka, ya watsa dukan Yahudawan da suke tare da kai, har sauran Yahudawan da suka ragu su halaka.”

16. Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohenan ɗan Kareya, “Kada ka kuskura ka yi wannan abu, gama ƙarya ce kake yi wa Isma'ilu.”

Irm 40