Irm 33:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Wannan wuri wanda yake kufai, inda ba mutum ko dabba, da cikin dukan biranensa, zai sāke zama makiyaya, inda masu kiwo za su zauna da garkunansu.

13. A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da suke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji.

14. “Ga shi, kwanaki suna zuwa sa'ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra'ila da na Yahuza.

15. A waɗannan kwanaki da a lokacin nan, zan sa wani reshe mai adalci ya fito daga zuriyar Dawuda, zai aikata gaskiya da adalci a ƙasar.

16. A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, ‘Adalcinmu Ubangiji ne.’

17. Gama ni Ubangiji na ce Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra'ila ba.

18. Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”

Irm 33