Irm 32:30-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.

31. Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana.

32. Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima.

33. Sun juya mini baya, ba su fuskance ni ba, ko da yake na yi ta koya musu, amma ba su saurara ga koyarwata ba.

34. Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin Haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi.

35. Sun gina wa Ba'al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”

Irm 32