Irm 31:21-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ki kafa wa kanki alamun hanya,Ki kafa wa kanki shaidu,Ki lura da gwadabe da kyau,Hanyar da kin bi, kin tafi.Ya budurwa Isra'ila, ki komo,Komo zuwa biranen nan naki.

22. Har yaushe za ki yi ta shakka,Ya ke 'yar marar bangaskiya?Gama Ubangiji ya halitta sabon abua duniya,Mace ce za ta kāre namiji.”

23. Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu.‘Ubangiji ya sa maka albarka,Ya wurin zaman adalci,Ya tsattsarkan tudu!’

24. Yahuza kuwa da dukan biranenta za su zauna tare a can, da manoma, da makiyaya, da garkunansu.

25. Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

Irm 31