Irm 30:14-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Dukan masu ƙaunarku sun mantada ku,Ba su ƙara kulawa da ku,Domin na yi muku bugu irin namaƙiyi.Na yi muku horo irin na maƙiyimarar tausayi,Domin laifofinku masu girma ne,Domin zunubanku da yawa suke.

15. Don me kuke kuka a kanrauninku?Ciwonku ba zai warke ba.Saboda laifofinku masu girma ne,Domin zunubanku da yawa suke,Shi ya sa na yi muku waɗannanabubuwa.

16. Domin haka dukan waɗanda sukacinye ku, za a cinye su,Dukan maƙiyanku, kowane ɗayansuzai tafi bauta,Waɗanda suka washe ku, za a washesu.Dukan waɗanda suka kwashe kuganima, su ma za a kwashe suganima.

17. Zan mayar muku da lafiyarku,Zan kuma warkar da raunukanku,Ko da yake maƙiyanku sunakiranku yasassu,Suna cewa, ‘Ai, Sihiyona ce, bawanda ya kula da ita.’Ni Ubangiji na faɗa.”

Irm 30