13. ya tafi ya faɗa wa Hananiya, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Ka karya karkiya ta itace, amma zan yi karkiya ta ƙarfe a maimakonta.
14. Gama haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa. Na sa wa wuyan dukan waɗannan al'ummai karkiya ta ƙarfe, don su bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila, za su kuwa bauta masa, gama na ba shi su, har da namomin jeji.’ ”
15. Sai annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka ji, ya Hananiya, Ubangiji bai aike ka ba, kana sa mutanen nan su dogara ga ƙarya.
16. Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”
17. A wannan shekara kuwa, a watan bakwai, sai annabi Hananiya ya mutu.