Irm 26:21-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sa'ad da sarki Yehoyakim, da dukan jarumawansa, da dukan sarakunansa suka ji maganarsa, sai sarki yana so ya kashe shi, amma sa'ad da Uriya ya ji, sai ya ji tsoro, ya gudu ya tsere zuwa Masar.

22. Sa'an nan sai sarki Yehoyakim ya aiki waɗansu mutane zuwa Masar, wato Elnatan ɗan Akbor da waɗansu tare da shi.

23. Suka kamo Uriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoyakim, sai ya sa aka kashe shi da takobi, aka binne gawarsa a makabartar talakawa.

24. Amma Ahikam ɗan Shafan yana tare da Irmiya, saboda haka ba a bashe shi ga mutane don su kashe shi ba.

Irm 26