Irm 26:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A farkon sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

2. “Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.

3. Mai yiwuwa ne su ji, har kowa ya juyo ya bar muguwar hanyarsa. Ni ma sai in janye masifar da na yi niyyar aukar musu da ita, saboda mugayen ayyukansu.”

Irm 26