1. Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.
2. A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu.
3. Sai Ubangiji ya ce mini, “Irmiya, me ka gani?”Sai na ce, “'Ya'yan ɓaure, akwai masu kyau ƙwarai, akwai kuma marasa kyau ƙwarai, har da ba za su ciwu ba.”
4. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini,