Irm 23:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Taku ta ƙare! Makiyayan da suka lalatar, suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji.

2. Haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya faɗa a kan makiyayan jama'arsa. “Kun warwatsar da garkena kun kore su, ba ku lura da su ba. Ni ma haka zan yi da ku saboda muguntarku, ni Ubangiji na faɗa.

3. Sa'an nan zan tattaro sauran garkena daga wuraren da aka warwatsa su, zan komo da su cikin garkensu, zan sa su hayayyafa su riɓaɓɓanya.

Irm 23