Irm 2:30-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Na hori 'ya'yanku, amma a banza, basu horu ba,Kun kashe annabawanku da takobikamar mayunwacin zaki.

31. Ya ku mutanen zamanin nan, kusaurari maganata.Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasarda take da kurama?Don me fa mutanena suke cewa,‘Mu 'yantattu ne,Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?

32. Budurwa ta manta da kayankwalliyarta?Ko kuwa amarya ta manta da kayanadonta?Amma mutanena sun manta da nikwanaki ba iyaka.

33. Kun sani sarai yadda za ku yi kufarauci masoya,Har mugayen mata ma, kun koyamusu hanyoyinku.

Irm 2