1. Ubangiji ya ce mini,
2. in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce,“Na tuna da amincinki a lokacinƙuruciyarki,Da ƙaunarki kamar ta amarya daango.Yadda kika bi ni a cikin jeji, da aƙasar da ba a shuka ba.
3. Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji,Nunar fari ta girbina.Dukan waɗanda suka ci daga cikinkisun yi laifi,Masifa za ta auko miki.Ni Ubangiji, na faɗa.”
4. Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra'ila.
5. Ubangiji ya ce,“Wane laifi ne na yi wa kakanninku,Da suka bar bina?Suka bauta wa gumaka marasaamfani,Su kuma suka zama marasa amfani.
6. Ba su kula da ni ba,Ko da yake na cece su daga ƙasarMasar.Na bi da su a cikin hamada,A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai,Busasshiya mai yawan hatsari,Ba a bi ta cikinta,Ba wanda yake zama cikinta kuma.