6. Saboda haka rana tana zuwa da ba za a ƙara ce da wannan wuri Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a ce da shi Kwarin Kisa.
7. A wannan wuri zan wofinta dabarun Yahuza da na Urushalima, zan sa a kashe jama'arsu da takobi, a gaban abokan gābansu, ta hannun waɗanda suke neman ransu. Zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.
8. Zan mai da wannan birni abin ƙyama, abin raini, dukan wanda ya wuce wurin zai yi mamaki, ya yi tsaki saboda dukan masifun da suka auka wa birnin.