20. Ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuza, da dukan Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.
21. Haka Ubangiji ya ce, ku yi hankali saboda rayukanku, kada ku ɗauki kaya a ranar Asabar, ko ku shigar da kowane abu ta ƙofofin Urushalima.
22. Kada ku ɗauki kaya, ku fita da shi daga gidajenku a ranar, ko ku yi kowane irin aiki, amma ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarci kakanninku.’
23. Amma duk da haka ba su kasa kunne, ko su mai da hankali ba. Amma suka taurare don kada su ji, su karɓi koyarwa.