15. Ga shi, suna ce mini,“Ina maganar Ubangiji take?Ta zo mana!”
16. Amma ni ban yi gudun zamanmakiyayi a gabanka ba,Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba,Ka kuwa sani.Abin da ya fito daga bakina kuwa,A bayyane yake gare ka.
17. Kada ka zamar mini abin razana,Kai ne mafakata cikin ranar masifa,
18. Bari waɗanda suka tsananta mini susha kunya,Amma kada ka bar ni in kunyata.Bari su tsorata,Amma kada ka bar ni in tsorata.Ka aukar musu da ranar masifa,Ka hallaka su riɓi biyu!
19. Haka Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Biliyaminu, wadda sarakunan Yahuza suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukan ƙofofin Urushalima.
20. Ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuza, da dukan Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.
21. Haka Ubangiji ya ce, ku yi hankali saboda rayukanku, kada ku ɗauki kaya a ranar Asabar, ko ku shigar da kowane abu ta ƙofofin Urushalima.