Irm 13:18-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ubangiji ya ce wa Irmiya,“Ka faɗa wa sarki da sarauniya,uwarsa, su sauka daga gadonsarautarsu,Domin an tuɓe kyakkyawan rawaninsarautarsu daga kansu.

19. An kulle biranen Negeb,Ba wanda zai buɗe su,Yahuza duka an kai ta zaman dole,Dukanta an kai ta zaman dole.

20. “Ku ta da idanunku, ku ga waɗandasuke zuwa daga arewa!Ina kyakkyawan garken nan da akaba ku?

21. Me za ku ce sa'ad da aka naɗa mukushugabanni,Waɗanda ku da kanku kuka koyamusu, suka zama abokanku?Ashe, azabai ba za su auko muku baKamar yadda sukan auko wa macemai naƙuda?

22. Idan kun ce a zuciyarku,‘Me ya sa waɗannan abubuwa sukasame mu?’Saboda yawan zunubanku ne,Shi ya sa an tone tsiraicinku,Aka wahalshe ku.

Irm 13