13. Gama yawan gumakansu sun kai yawan biranensu. Yawan bagadan da suke da su kuma sun kai yawan titunan Urushalima, abin kunya, bagadan ƙona wa Ba'al turare ne.’
14. Don haka kada ka yi wa waɗannan mutane addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, gama ba zan kasa kunne gare su ba, ko da sun yi kirana a lokacin wahalarsu.”
15. Ubangiji ya ce, “Wane iko ƙaunatacciyata take da shi cikin Haikalina, da ya ke ta aikata mugayen ayyuka? Ko alkawarai da naman hadayu za su iya kawar miki da ƙaddararki, har da za ki yi taƙama?
16. Dā na kira ki itacen zaitun mai duhuwa, kyakkyawa, mai kyawawan 'ya'ya, amma da ƙugin babbar iska za a cinna miki wuta, za ta kuwa cinye rassanki.”