Gal 6:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.

2. Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu.

3. Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan.

4. Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa'an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.

5. Lalle kowa yă ji da kayansa.

6. Duk wanda aka koya wa Maganar, yă ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.

7. Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.

8. Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami.

9. Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.

10. To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.

11. Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da nake muku da hannuna!

Gal 6