7. Cikin girman ɗaukakarka, ka kā da maƙiyanka, ka aika da hasalarka,Ka cinye su kamar ciyawa.
8. Da hucin numfashin hancinka ruwa ya tattaru,Rigyawa ta tsaya kamar tudu,Zurfafan ruwa suka daskare a tsakiyar bahar.
9. Magabcin ya ce, ‘Zan bi, in kama su, in raba ganima,Muradina a kansu zai biya, zan zare takobina, hannuna zai hallaka su.’
10. Ka hura iskarka, bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.
11. “Ya Ubangiji, wane ne kamarka a cikin alloli?Wa yake kamarka a cikin ɗaukaka da tsarki?Mai banrazana cikin mafifitan ayyuka, mai aikata mu'ujizai.
12. Ka miƙa dantsen damanka, ƙasa ta haɗiye su.
13. Da tabbatacciyar ƙaunarka, ka bi da jama'arka da ka fansa,Ka bi da su da ƙarfinka zuwa tsattsarkan mazauninka.
14. Al'ummai suka ji suka yi rawar jiki,Tsoro ya kama mazaunan Filistiya.
15. Sarakunan Edom suka tsorata,Shugabannin Mowab suna rawar jiki,Dukan mazaunan Kan'ana sun narke.
16. Tsoro da razana sun aukar musu,Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse,Har jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,I, jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,
17. Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka,Wurin, ya Ubangiji, da ka maishe shi tsattsarkan mazauninka,Tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, wanda ka kafa da ikonka.
18. Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”
19. Gama sa'ad da dawakan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa suka shiga bahar, Ubangiji ya komar da ruwan bahar a bisansu, amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busassiyar ƙasa ta tsakiyar bahar.
20. Sai Maryamu, annabiya, 'yar'uwar Haruna, ta ɗauki kuru cikin hannunta. Mata duka suka fita, suka bi ta da kuwaru suna ta rawa.
21. Maryamu tana raira musu waƙa tana cewa,“Raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara,Doki da mahayinsa, ya jefar cikin bahar.”
22. Musa kuwa ya bi da Isra'ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba.
23. Sa'ad da suka zo Mara, sun kasa shan ruwan Mara saboda ɗacinsa, don haka aka sa masa suna Mara.