Far 7:14-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi.

15-16. Su waɗanda suka shiga, namiji ne da ta mace na kowane taliki, suka shiga jirgin kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya.

17. Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba'in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya.

18. Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye.

19. Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da yake ƙarƙashin sammai duka.

20. Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar.

21. Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum,

22. da kowane abin da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu.

23. Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.

24. Ruwa kuma ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.

Far 7