Far 49:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa.

2. “Ku taru ku ji, ya ku 'ya'yanYakubu, maza,Ku kuma kasa kunne ga Isra'ilamahaifinku.

3. “Ra'ubainu, kai ɗan farinane, ƙarfina,Ɗan balagata, isasshe kuma, mafiƙarfi duka cikin 'ya'yana.

4. Kamar ambaliyar ruwa mai fushikake,Amma ba za ka zama mafi darajaba,Domin ka hau gadon mahaifinka,Sa'an nan ka ƙazantar da shi.

5. “Saminu da Lawi 'yan'uwa ne,Suka mori takubansu cikin ta dahankali.

Far 49