Far 48:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “'Ya'yana ne maza waɗanda Allah ya ba ni a nan.”Sai ya ce, “Kawo su gare ni, ina roƙonka, domin in sa musu albarka.”

10. Yanzu fa, idanun Isra'ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su.

11. Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na 'ya'yanka.”

12. Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra'ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa.

13. Yusufu ya ɗauki su biyu ɗin, Ifraimu a hannunsa na dama zuwa hannun hagun Isra'ila, Manassa kuma a hannunsa na hagu zuwa dama na Isra'ila, ya kawo su kusa da shi.

Far 48