Far 43:7-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan'uwa?’ Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, ‘Ku zo da ɗan'uwanku’?”

8. Sai Yahuza ya ce wa Isra'ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu.

9. Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada,

10. gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.”

11. Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure.

12. Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi.

13. Ku kuma ɗauki ɗan'uwanku, ku tashi ku sāke komawa wurin mutumin.

14. Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan'uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”

15. Sai mutane suka ɗauki tsarabar, suka kuma ɗauki riɓin kuɗin a hannunsu tare da Biliyaminu. Suka tashi suka gangara zuwa Masar, suka shiga wurin Yusufu.

16. Sa'ad da Yusufu ya ga Biliyaminu tare da su, ya faɗa wa mai hidimar gidansa, ya ce, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.”

17. Mutumin kuwa ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa, ya shigo da mutanen a gidan Yusufu.

18. Mutanen suka tsorata sabili da an kawo su a cikin gidan Yusufu, sai suka ce, “Ai, saboda kuɗin da aka mayar mana cikin tayakanmu a zuwanmu na farko, shi ya sa aka shigar da mu, domin ya nemi hujja a kanmu, ya fāɗa mana, ya maishe mu bayi, ya kuma ƙwace jakunanmu.”

19. Sai suka hau wurin mai hidimar gidan Yusufu, suka yi magana da shi a ƙofar gida,

20. suka ce, “Ya shugaba, mun zo a karo na farko sayen abinci,

21. amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin kowannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su,

22. ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.”

Far 43