4. Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.
5. Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin 'ya'yan Yakubu.
6. Sai Yakubu ya zo Luz, wato Betel, wadda take cikin Kan'ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi.
7. A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa'ad da yake guje wa ɗan'uwansa.
8. Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut.
9. Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka.
10. Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra'ila.” Don haka aka kira sunansa Isra'ila.