5. ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni.
6. Kun sani na yi wa mahaifinku barantaka da dukan ƙarfina,
7. duk da haka mahaifinku ya cuce ni, ya yi ta sassauya ladana har sau goma, amma Allah bai ba shi ikon zambatata ba.
8. In ya ce, ‘Dabbare-dabbare, su ne ladanka,’ duk garken sai ya haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce ‘masu sofane ne ladanka,’ sai garken duka ya haifi masu sofane.
9. Ta haka Allah ya kwashe dukiyar mahaifinku ya ba ni.
10. “A lokacin ɗaukar cikin garke, cikin mafarki na ta da idanuna, na kuwa gani cikin mafarkin, bunsuran da suke hawan garken, masu sofane, da dabbare-dabbare da roɗi-roɗi ne.
11. Sai mala'ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, ‘Yakubu,’ sai na ce, ‘Ga ni.’
12. Ya kuwa ce, ‘Ta da idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan awaki masu sofane ne, dabbare-dabbare da roɗi-roɗi, gama na ga dukan abin da Laban yake yi maka.
13. Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”
14. Rahila da Lai'atu suka amsa masa, “Akwai wani rabo, ko gādon da ya rage mana a cikin gidan mahaifinmu?
15. Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu.
16. Dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga wurin mahaifinmu, tamu ce da 'ya'yanmu, yanzu fa, kome Allah ya faɗa maka, sai ka yi.”
17. Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki 'ya'yansa, da matansa a bisa raƙumansa,
18. ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mahaifinsa Ishaku.
19. Amma a sa'an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.