9. Kafin ya rufe baki, sai ga Rahila ta zo da bisashen mahaifinta, gama ita take kiwonsu.
10. Sa'ad da Yakubu ya ga Rahila, 'yar Laban kawunsa, da bisashen, sai Yakubu ya hau ya kawar da dutsen daga bakin rijiyar, ya shayar da garken Laban, kawunsa.
11. Yakubu kuwa ya sumbaci Rahila, ya fara kuka da ƙarfi.
12. Ya faɗa mata shi dangin mahaifinta ne, shi kuma ɗan Rifkatu ne, sai ta sheƙa ta faɗa wa mahaifinta.
13. Sa'ad da Laban ya sami labari a kan Yakubu ɗan 'yar'uwarsa, sai ya sheƙo ya tarye shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kawo shi a gidansa. Yakubu ya labarta wa Laban al'amura duka.
14. Laban ya ce masa, “Hakika, kai ƙashina ne da namana!” Yakubu ya zauna wata guda tara da Laban.
15. Laban kuwa ya ce wa Yakubu, “Don kana dangina, za ka yi mini barantaka a banza? Ka faɗa mini, nawa zan biya ka?”
16. Laban dai yana da 'ya'ya mata biyu, sunan babbar Lai'atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.
17. Lai'atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.
18. Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin 'yarka Rahila.”
19. Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.”
20. Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.
21. Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.”
22. Sai Laban ya tattara mutanen wurin duka, ya yi biki.
23. Amma da maraice, ya ɗauki 'yarsa Lai'atu ya kawo ta wurin Yakubu, Yakubu ya shiga a wurinta.