Sa'ad da Laban ya sami labari a kan Yakubu ɗan 'yar'uwarsa, sai ya sheƙo ya tarye shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kawo shi a gidansa. Yakubu ya labarta wa Laban al'amura duka.