35. Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.
36. Saratu ta haifa wa maigidana ɗa cikin tsufanta, a gare shi kuma ya ba da dukan abin da yake da shi.
37. Maigidana ya rantsar da ni da cewa, ‘Ba za ka auro wa ɗana mace daga cikin 'ya'yan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a ƙasarsu ba,
38. amma ka tafi gidan mahaifina da dangina, ka auro wa ɗana mace.’
39. Sai na ce wa maigidana, ‘Watakila matar ba za ta biyo ni ba.’
40. Amma ya amsa mini ya ce, ‘Ubangiji wanda nake tafiya a gabansa zai aiki mala'ikansa tare da kai, ya arzuta hanyarka, za ka kuwa auro wa ɗana mace daga cikin dangina daga gidan mahaifina.
41. Sa'an nan za ka kuɓuta daga rantsuwata. Sa'ad da ka zo wurin dangina, idan kuwa ba su ba ka ita ba, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’
42. “Yau kuwa da na iso bakin rijiyar, sai na ce a raina, ‘Ya Ubangiji, Allah na shugabana Ibrahim, in nufinka ne ka arzuta tafiyata.
43. Ga ni, ina tsaye a bakin rijiyar kuwa, bari budurwar da za ta fito ɗibar ruwa, wadda in na ce mata, “Roƙo nake, ba ni ruwa kaɗan daga ruwan tulunki in sha,”
44. in ta amsa mini, “To, sha, zan ɗebo wa raƙumanka kuma,” bari ta zama ita ce wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’
45. Kafin in gama tunani a zuciyata, sai ga Rifkatu ta fito ɗauke da tulun ruwa a kafaɗarta, ta gangara zuwa rijiya ta ɗebo. Na ce mata, ‘Roƙo nake, ki ba ni, in sha.’
46. Nan da nan ta sauke tulunta daga kafaɗarta, ta ce, ‘To, sha, zan kuma shayar da raƙumanka.’ Na sha, ta kuma shayar da raƙuman.
47. Na kuwa tambaye ta, ‘'Yar gidan wane ne ke?’ Ta ce, ‘Ni 'yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ Sai na sa mata zobe a hanci, mundaye kuma a hannu.
48. Sa'an nan na yi ruku'u, na yi wa Ubangiji sujada, na yabi Ubangiji Allah na maigidana, Ibrahim, wanda ya bishe ni a hanya sosai, in auro wa ɗansa 'yar danginsa.
49. Yanzu fa, idan za ku amince ku gaskata da maigidana, ku faɗa mini, in ba haka ba, sai ku faɗa mini, domin in san abin yi, in juya dama ko hagu.”
50. Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al'amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a'a.
51. Ga Rifkatu nan gabanka, ka ɗauke ta ku tafi, ta zama matar ɗan maigidanka, bisa ga faɗar Ubangiji.”