4. A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa.
5. Ibrahim ya ce wa samarinsa, “Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa'an nan mu komo wurinku.”
6. Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare.
7. Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba!”Sai ya ce, “Ga ni, ɗana.”Ya ce, “Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?”
8. Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare.