6. Ibrahim kuwa ya gaggauta zuwa cikin alfarwa wurin Saratu, ya ce, “Ki shirya mudu uku na gari mai laushi da sauri, ki cuɗa, ki yi waina.”
7. Sai Ibrahim ya sheƙa zuwa garke, ya ɗauki maraƙi, matashi mai kyau, ya ba baransa, ya kuwa shirya shi nan da nan.
8. Ya ɗauki kindirmo da madara, da maraƙin da ya shirya, ya ajiye a gabansu, ya tsaya kusa da su a gindin itacen a sa'ad da suke ci.
9. Suka ce masa, “Ina Saratu matarka?”Ya ce, “Tana cikin alfarwa.”
10. Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne.
11. Ga shi kuwa, Ibrahim da Saratu sun tsufa, sun kwana biyu, gama Saratu ta daina al'adar mata.
12. Sai Saratu ta yi dariya a ranta, tana cewa, “Bayan na tsufa mai gidana kuma ya tsufa sa'an nan zan sami wannan gatanci?”
13. Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya, har da ta ce, ‘Ashe zan haifi ɗa, a yanzu da na riga na tsufa?’
14. Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”
15. Amma Saratu ta yi mūsu, tana cewa, “Ai, ban yi dariya ba,” Gama tana jin tsoro.Ya ce, “A'a, hakika kin yi dariya.”
16. Sai mutanen suka tashi daga wurin, suka fuskanci Saduma, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya ya sallame su.
17. Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin aikatawa?
18. Ga shi kuwa, Ibrahim zai ƙasaita ya zama al'umma mai iko, sauran al'umman duniya duka za su sami albarka ta dalilinsa.
19. Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.
20. Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai,