2-14. Gershom shi ne shugaban iyalin Finehas,Daniyel shi ne na iyalin Itamar,Hattush ɗan Shekaniya, shi ne na iyalin Dawuda.Zakariya shi ne na iyalin Farosh, ya zo da iyalinsa mutum ɗari da hamsin.Eliyehoyenai ɗan Zarahiya, shi ne na iyalin Fahat-mowab, tare da shi kuma akwai mutum ɗari biyu.Shekaniya ɗan Yahaziyel, shi ne na iyalin Zattu, tare da shi akwai mutum ɗari uku.Ebed ɗan Jonatan, shi ne na iyalin Adin, tare da shi akwai mutum hamsin.Yeshaya ɗan Ataliya, shi ne na iyalin Elam, yana tare da mutum saba'in.Zabadiya ɗan Maikel, shi ne na iyalin Shefatiya, yana tare da mutum tamanin.Obadiya ɗan Yehiyel, shi ne na iyalin Yowab, yana tare da mutum ɗari biyu da goma sha takwas.Shelomit ɗan Yosifiya, shi ne na iyalin Bani, yana tare da mutum ɗari da sittin.Zakariya ɗan Bebai, shi ne na iyalin Bebai, yana tare da mutum ashirin da takwas.Yohenan ɗan Hakkatan, shi ne na iyalin Azgad, yana tare da mutum ɗari da goma.Elifelet, da Yehiyel, da Shemaiya, su ne na iyalin Adonikam (su ne suka zo daga baya), suna tare da mutum sittin.Utai da Zabbud, su ne na iyalin Bigwai, suna tare da mutum saba'in.
20. Da kuma ma'aikatan Haikali mutum ɗari biyu da ashirin, waɗanda Dawuda da ma'aikatansa suka keɓe domin su taimaki Lawiyawa. Aka ambaci waɗannan da sunayensu.
21. Na kuma yi shelar azumi a bakin rafin Ahawa don mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu roƙe shi ya kiyaye mu, da 'ya'yanmu, da kayanmu a hanya.
22. Gama na ji kunya in roƙi sarki ya ba mu sojojin ƙasa da na doki su kāre mu daga maƙiya a hanya, da yake na riga na faɗa masa cewa, “Allah yana tare da dukan waɗanda suke nemansa, ikonsa da fushinsa mai zafi kuwa yana kan dukan waɗanda suke mantawa da shi.”
23. Don haka muka yi azumi, muka roƙi Allah saboda wannan, shi kuwa ya ji roƙonmu.
24. Sai na keɓe goma sha biyu daga cikin manyan firistoci, wato Sherebiya, da Hashabiya, da waɗansu goma daga cikin danginsu.