20. Da kuma ma'aikatan Haikali mutum ɗari biyu da ashirin, waɗanda Dawuda da ma'aikatansa suka keɓe domin su taimaki Lawiyawa. Aka ambaci waɗannan da sunayensu.
21. Na kuma yi shelar azumi a bakin rafin Ahawa don mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu roƙe shi ya kiyaye mu, da 'ya'yanmu, da kayanmu a hanya.
22. Gama na ji kunya in roƙi sarki ya ba mu sojojin ƙasa da na doki su kāre mu daga maƙiya a hanya, da yake na riga na faɗa masa cewa, “Allah yana tare da dukan waɗanda suke nemansa, ikonsa da fushinsa mai zafi kuwa yana kan dukan waɗanda suke mantawa da shi.”