8. Ezra kuma tare da su, suka iso Urushalima a watan biyar na shekara ta bakwai ta sarautar sarkin.
9. Suka taso daga Babila a rana ta fari ga watan fari, suka iso Urushalima a rana ta fari ga watan biyar, Allah kuwa yana tare da su.
10. Gama Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra'ilawa dokoki da farillan Allah.
11. Wannan ita ce takardar doka da sarki Artashate ya ba Ezra, wanda yake firist da magatakarda, ƙwararre cikin sha'anin dokoki da umarnan Ubangiji a cikin Isra'ilawa.
12. Ta ce, “Daga Artashate, sarkin sarakuna, zuwa ga Ezra firist, masanin shari'ar Allah na Sama.