11. To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra'ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.
12. Amma saboda kakanninmu suka tsokani Allah na Sama, sai ya bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, mutumin Kaldiya. Shi ne ya lalatar da Haikalin nan, ya kuma kwashe jama'a zuwa Babila.
13. Amma a shekara ta fari ta sarautar Sairus, Sarkin Babila, sai ya ba da izini a sāke gina wannan Haikali na Allah.
14. Kwanonin zinariya da na azurfa na Haikalin Allah, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga cikin Haikalin da yake Urushalima, zuwa haikalin gumaka na Babila, sarki Sairus ya ɗauke su daga haikalin Babila ya ba wani mai suna Sheshbazzar wanda ya naɗa shi mai mulki.