5. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka, ka duba wajen arewa.” Na kuwa ɗaga idanuna wajen arewa, na kuma ga siffa ta tsokano kishi a mashigin ƙofar bagade na wajen arewa.
6. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwa masu banƙyama da mutanen Isra'ila suke yi a nan don su kore ni nesa da Haikalina? Ai, za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka.”
7. Ya kuma kai ni ƙofar shirayi. Sa'ad da na duba, sai ga wani rami a bangon.
8. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka haƙa bangon.” Da na haƙa bangon, sai ga ƙofa.
9. Ya ce, mini, “Ka shiga ka ga abubuwan banƙyama da suke aikatawa a nan.”
10. Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra'ila kewaye da bangon.
11. Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.