4. Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.
5. Yankin Ifraimu yana kusa da yankin Manassa daga gabas zuwa yamma.
6. Yankin Ra'ubainu yana kusa da yankin Ifraimu daga gabas zuwa yamma.
7. Yankin Yahuza yana kusa da yankin Ra'ubainu daga gabas zuwa yamma.
8. “Kusa da yankin Yahuza daga gabas zuwa yamma, sai yankin da za ku keɓe. Faɗinsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], tsawonsa kuma daidai da tsawon yankunan kabilai daga gabas zuwa yamma. Haikali zai kasance a tsakiyar yankin.
9. “Yankin da za ku keɓe wa Ubangiji, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000].
10. Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma [10,000] ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma [10,000], a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000]. Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa.
11. Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci daga zuriyar Zadok waɗanda suka kiyaye umarnina, ba su karkace kamar yadda Lawiyawa suka yi lokacin da jama'ar Isra'ila suka karkace ba.
12. Zai zama rabonsu daga tsattsarkan yankin ƙasar da take kusa da yankin Lawiyawa.
13. Gab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuma kamu dubu goma [10,000]. Tsawonsa duka zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuwa kamu dubu goma [10,000].
14. Daga cikinsa ba za su sayar ba, ko su musayar, ba kuma za su jinginar da wannan keɓaɓɓen yankin ƙasa ba, gama tsattsarka ne na Ubangiji.
15. “Ragowar yankin mai faɗin kamu dubu biyar [5,000], da tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], zai zama hurumin birnin, inda za a yi gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar yankin.
16. Ga yadda girman birnin zai kasance, a wajen arewa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen kudu kuwa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen gabas kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen yamma kuma kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500].
17. Birnin zai kasance da hurumi a kewaye da shi. A wajen gabas kamu metan da hamsin, a wajen yamma kamu metan da hamsin, a wajen kudu kamu metan da hamsin, a wajen arewa kuma kamu metan da hamsin.
18. Ragowar tsawon yankin da yake gab da tsattsarkan yankin, zai zama kamu dubu goma [10,000] a wajen gabas, a wajen yamma kamu dubu goma [10,000]. Amfanin da yankin zai bayar, zai zama abincin ma'aikatan birnin.