Ez 35:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Zan mai da Dutsen Seyir kufai marar amfani. Zan kashe duk mai shiga ko mai fita a cikinsa.

8. Zan cika duwatsunsa da gawawwaki. Waɗanda za a kashe da takobi za su faɗi a kan tuddansa, da cikin kwarurukansa, da cikin dukan kwazazzabansa.

9. Zan maishe shi kufai marar amfani har abada. Ba wanda zai zauna a cikin biranensa. Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.

10. “Da yake ya ce al'umman nan biyu, da ƙasashen nan biyu za su zama nasa, ya mallake su, ko da yake Ubangiji yana cikinsu,

11. domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, hakika zan saka masa gwargwadon fushinsa, da kishinsa, da ƙiyayyar da ya nuna musu. Zan sanar da kaina a gare su sa'ad da na hukunta shi.

12. Zai sani Ubangiji ne wanda ya ji dukan zarge zargen da ya yi wa duwatsun Isra'ila, da ya ce, ‘An maishe su kufai marar amfani, an ba mu su mu cinye!’

13. Na ji tsiwa da dukan surutan da ya yi mini.

14. “Ni Ubangiji Allah zan maishe shi kufai marar amfani, domin dukan duniya ta yi farin ciki.

Ez 35