Zan ƙarfafa hannuwan Sarkin Babila, amma hannuwan Fir'auna za su shanye. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sa takobina a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai miƙe shi a kan ƙasar Masar.