Ez 30:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce Ubangiji Allah ya ce maka ka yi kuka, kana cewa,‘Kaito, kaito saboda wannan rana!’

3. Gama ranar ta gabato,Ranar Ubangiji ta yi kusa,Rana ce ta gizagizai,Ranar halakar al'ummai.

4. Takobi zai fāɗa a kan Masar,Azaba kuma za ta sami Habasha.Za a kashe mutane a Masar,Za a kwashe dukiyarta,A rushe harsashin gininta.

5. “Yaƙi zai ci Habasha, da Fut, da Lud, da dukan Arabiya, da Libya, da mutanen ƙasar da suka haɗa kai da su.”

6. Ubangiji ya ce,“Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi.Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare.Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.

7. Za ta zama kufai fiye da sauran ƙasashe,Biranenta kuma za su zama kufai, marar amfani, fiye da sauran birane.

8. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji,Sa'ad da na kunna wuta cikin Masar,Na kuma kakkarya dukan masu taimakonta.

9. “A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”

10. Ubangiji Allah ya ce,“Zan sa dukiyar Masar ta ƙareTa hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila,

11. Shi da mutanensa,Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al'umma,Za a kawo su don su hallakar da ƙasar.Za su zare takubansu a kan Masar,Su cika ƙasar da gawawwaki.

Ez 30