Ez 3:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ga shi, na sa fuskarka da goshinka su zama da tauri kamar nasu.

9. Kamar yadda lu'ulu'u ya fi ƙanƙarar dutse ƙarfi, haka nan na sa goshinka ya zama. Kada ka ji tsoronsu, ko kuwa ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.”

10. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, sai ka ji, ka karɓi dukan maganata da zan faɗa maka.

11. Sa'an nan ka tafi wurin mutanenka waɗanda suke cikin bautar talala, ka faɗa musu, ko su ji, ko kada su ji.”

12. Sa'an nan Ruhu ya ɗaga ni, sai na ji murya a bayana, kamar babban motsi, tana cewa, “Yabo ga ɗaukakar Ubangiji a kursiyinsa.”

13. Na kuma ji amon fikafikan talikan ne sa'ad da suka taɓa junansu, da kuma amon ƙafafun da suke kusa da talikan, da amon babban motsi.

14. Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi.

15. Na zo wurin 'yan bautar talala a Telabib, waɗanda suke bakin kogin Kebar. Na zauna tare da su kwana bakwai, ina ta mamaki.

16. A ƙarshen kwana bakwai ɗin, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

17. “Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra'ila. Sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina.

18. Idan na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ kai kuwa ba ka faɗakar da shi a kan mugayen ayyukansa don ka ceci ransa ba, wannan mugun mutum zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

Ez 3