15. Na zo wurin 'yan bautar talala a Telabib, waɗanda suke bakin kogin Kebar. Na zauna tare da su kwana bakwai, ina ta mamaki.
16. A ƙarshen kwana bakwai ɗin, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
17. “Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra'ila. Sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina.
18. Idan na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ kai kuwa ba ka faɗakar da shi a kan mugayen ayyukansa don ka ceci ransa ba, wannan mugun mutum zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.
19. Amma idan ka faɗakar da mugu, ya kuwa ƙi barin muguntarsa, zai mutu cikin zunubinsa, kai kam ka kuɓuta.