19. Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Zan ba Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ƙasar Masar, zai kwashe dukiyarta, ya lalatar da ita, ya washe ta ganima. Za ta zama abin biyan sojojinsa.
20. Na ba shi ƙasar Masar saboda wahalar da ya sha, gama ni suka yi wa aiki. Ni Ubangiji Allah na faɗa.
21. “A ranan nan zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda ya zama babban sarki, zan kuma buɗe bakinka a tsakiyarsu. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”