Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Zan ba Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ƙasar Masar, zai kwashe dukiyarta, ya lalatar da ita, ya washe ta ganima. Za ta zama abin biyan sojojinsa.